Farfesa Abubakar babban na hannun-daman tsohon
gwamnan jihar Rabi'u Musa Kwankwaso ne.
Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa ranar Laraba zai
bayyana dalilansa na ficewa daga jam'iyyar.
Sai dai a wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na
mazabarsa ta Mandawari, Farfesa Abubakar, ya ce ya fita
daga jam'iyyar ne domin radin kansa.
A watan Agusta ya sauka daga kujerar mataimakin
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sannan ya fice daga
jam'iyyar APC ya koma PDP inda uban gidansa, Sanata
Kwankwaso yake.
A wancan lokacin, Farfesa Hafiz Abubakar ya ce ya fita
daga APC ne saboda gwamnan jihar yana barazana ga
rayuwarsaSai dai daga bisani ya koma PDP inda ya nemi tsayawa
takarar gwamnan jihar a inuwar jam'iyyar.
Zabukan fitar da gwanin da aka yi a jam'iyyar reshen jihar
Kano sun bar baya da kura sakamakon tsayar da Malam
Abba Yusuf - surukin Sanata Kwankwaso - a matsayin
mutumin da zai yi takarar gwamna a PDP.
Rahotanni sun ce wannan mataki bai yi wa wasu jiga-jigan
jam'iyyar a jihar dadi ba, cikinsu har da Farfesa Abubakar,
wanda ya yi tsammani shi za a tsayar a matsayin dan
takara.
Fitar sa daga jam'iyyar ta PDP ka iya kawo mata matsala a
zabukan 2019 musamman saboda da matsayinsa na
mutumin da a baya ba ya jayayya ga duk matakin da
tsohon gwamnan jihar ya dauka.

0 comments Blogger 0 Facebook

Post a Comment

 
gaskiya24 © 2013. All Rights Reserved. Share on Themes24x7. Powered by Blogger
Top

Powered by themekiller.com