Wani shugban kungiyar, Abdullahi Muhammad ya
ce harin da jami'an tsaro ke kai musu ba zai hana
su cigaba ba
- Ya ce muddin jami'an tsaron ne da harsasai da za
suyi asara, 'yan kungiyar suna da kirjin karbar
hasasanA jiya, Talata ne 'yan Kungiyar Ismlamic
Movement of Nigeria (IMN) suka bayyana cewa
ba za su taba dena tattakin da su ka fara a
Abuja ba har sai lokacin da gwamnati ta sako
shugabansu Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da
matarsa daga inda ake tsare su tun shekarar
2015.
Bayan artabun da su kayi da jami'an tsaro,
daya daga cikin shugabanin kungiyar,
Abdullahi Muhammad ya shaidawa manema
labarai cewa ba za su dena tattakin ba duk da
harin da jami'an tsaro ke kai Ya ce idan gwamnati na son su dena tattakin, su
saki shugabansu da matarsa da sauran
mambobin kungiyar da jami'an tsaro suka
tsare.
A cewarsa, "ba za mu dena tattakin ba har sai
lokacin da suka aikata abin da ya dace. Idan
suna so su cigaba da kashe mambobin mu, idan
suna da harsasai da za suyi asara, mu kuma
muna da kirgin karabar harsashen."
Kazalika, wata kungiyar kirista, Young Christian
Forun (YCF) reshen Abuja ta janyo hankalin
mutane kan artabun da jami'an tsaro keyi da
mabiya Shi'a a Abuja wanda ke janyo asarar
dukiya da rayyuka a Abuja.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

0 comments Blogger 0 Facebook
Post a Comment