Wata sanarwa da kakakin rundunar Mr Jomoh Moshood ya
aike wa manema labarai ta kara da cewa an kama mutanen
ne dauke da kwalabe 31 na bama-baman da aka hada da
fetur da muggan makamai.
A cewar sanarwar ana gudanar da bincike kan 'yan Shi'ar
kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban
kotu.
Mr Moshood ya zargi mabiyan Sheikh Ibrahim El-Zakzakky
da kona motocin 'yan sanda da tayar da hargitsi inda ya ce
babban sufeton 'yan sandan kasar ya ba da umarni ga 'yan
sanda su murkushe 'ya'yan kungiyar a dukkan inda suke a
fadin Najeriya."An sanya kwamishinonin 'yan sandan jihohin da akwai
mabiya kungiyar 'yan Uwa Musulmi ta El-Zakzakky da su
shiga cikin shirin ko-ta-kwana domin murkushe su kamar
yarda doka ta tanada sannan su hana 'yan kungiyar tayar
da kayar baya a jihohin," in ji sanarwar.
Tun daga karshen makon jiya ne dai mabiya El-Zakzakky
suka soma isa Abuja inda za su yi gangami na jimanin
mutuwar Hussain, jikan manzon Allah Annabi Muhammad
(SAW) wanda ake yi duk shekaraSai dai sun yi zargin cewa jami'an tsaro sun hana su shiga
lamarin da ya haddasa arangama tsakaninsu har aka yi
asarar rayuka.
Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ranar Litinin
ta ce an kashe mabiya Shi'a uku yayin da sojoji suka jikkata
akamakon taho-mu-gamar da aka yi a tsakaninsu.
Sanarwar ta ce 'yan Shi'a sun far wa dakarunta da ke
sanya ido a wuraren binciken ababen hawa da ke gadar
Kugbo/Karu.
"Mabiya mazahabar wadanda ke da matukar yawa sun
kutsa kai ta shingen binciken ababen hawa inda suka
turmushe 'yan sanda.
"Daga nan ne 'yan sandan suka janye inda suka shiga cikin
sojojin da ke yunkurin dakile harbe-harben da mutanen ke
yi," in ji sanarwar.
Ta kara da cewa "lokacin arangamar ne mabiya mazahabar
uku suka mutu san nan soji hudu suka jikkata, inda aka tura
su asibiti domin karbar magani."
Amma 'yan Shi'a sun ce jami'an tsaron Najeriya sun kashe
mambobinsu 24.
Masu sharhi sun shaida wa BBC cewa ya kamata gwamnati
da mabiya mazhabar Shi'a su sasanta tsakaninsu domin
gujewa abin da ka-je-ya-komo.

0 comments Blogger 0 Facebook

Post a Comment

 
gaskiya24 © 2013. All Rights Reserved. Share on Themes24x7. Powered by Blogger
Top

Powered by themekiller.com